All Islam Library

96 - The Clot - Al-`Alaq

:1

Ka yi karatu da sunan Ubangijinka, wanda Ya yi halitta.

:2

Ya hahitta mutum daga gudan jini.

:3

Ka yi karatu, kuma UbangiJinka shi ne Mafi karimci.

:4

Wanda Ya sanar (da mutum) game da alƙalami.

:5

Ya sanar da mutum abin da bai sani ba.

:6

A'aha! Lalle, ne mutum haƙĩƙa, yana girman kai (ya ƙi karatu).

:7

Dõmin yã ga kansa, yã wadãta.

:8

Lalle ne zuwa ga Ubangijinka makoma take.

:9

Shin, kã ga wanda ke hana.

:10

Bãwã idan yã yi salla?

:11

Ashe, kã gani, idan (shi bãwan) ya kasance a kan shiriya?

:12

Ko ya yi umurni da taƙawa?

:13

Ashe, kã gani, idan (shi mai hanin) ya ƙaryata, kuma ya jũya bãya?

:14

Ashe, bai sani ba cewa Allah Yanã gani?

:15

A'aha! Lalle ne, idan bai hanu ba, lalle ne zã Mu ja gãshin makwarkwaɗa.

:16

Makwarkwaɗa maƙaryaciya, mai laifi.

:17

Sai ya kirayi ƙungiyarsa.

:18

Zã Mu kirayi zabaniyãwa (mala'iku mãsu girma).

:19

A'aha kada ka bĩ shi. Kuma ka yi tawali'u, kuma ka nemi kusanta (zuwa ga Ubangijinka).