1
Lalle ne Mũ, Mun saukar da shi (Alƙur'ãni) a cikin Lailatul ƙadari (daren daraja)
2
To, me ya sanar da kai abin da ake cewa Lailatul ¡adari?
3
Lailatul ¡adari mafi alheri ne daga wasu watanni dubu.
4
Mala'iku da Rũhi suna sauka a cikinsa da iznin Ubangijinsu sabõda kowane umurni.
5
Sallama ne shi daren, har fitar alfijiri.