All Islam Library
1

Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai.

2

Godiya ta tabbata ga Allah, Ubangijin halittu;

3

Mai rahama, Mai jin ƙai;

4

Mai nuna Mulkin Rãnar Sakamako.

5

Kai muke bauta wa, kuma Kai muke neman taimakonKa.

6

Ka shiryar da mu ga hanya madaidaiciya.

7

Hanyar waɗanda Ka yi wa ni'ima, ba waɗanda aka yi wa fushi ba, kuma ba ɓatattu ba.