1
Inã rantsuwa da Attinu da Azzaitũn.
2
Da Dũr Sĩnĩna.
3
Da wannan gari amintacce.
4
Lalle ne, Mun halitta mutum a cikin mafi kyawon tsayuwa.
5
Sa'an nan, Muka mayar da shi mafi ƙasƙantar masu rauni
6
Face waɗanda suka yi imani, kuma suka aikata ayyukan ƙwarai, saboda haka suna da sakamako wanda bã ya yankewa.
7
To, bãyan haka mẽ ya sanya ka ka ƙaryata sakamako (wanda za a yi a bãyan Tãshin ¡iyãma)?
8
Ashe Allah bã Shi ne Mafi mãsu hukunci kyãwon hukunci ba?