1
Ba Mu bũɗa maka zũciyarka ba (dõmin ɗaukar haƙuri da fahimta)?
2
Kuma Muka saryar maka da nauyinka, Ashe.
3
Wanda ya nauyayi bãyanka?
4
Kuma Muka ɗaukaka maka ambatonka?
5
To, lalle ne tãre da tsananin nan akwai wani sauƙi.
6
Lalle ne tãre da tsananin nan akwai wani sauƙi.
7
Sabõda haka idan ka ƙãre (ibãda) sai ka kafu (kana rõƙon Allah).
8
Kuma zuwa ga Ubangijinka ka yi kwaɗayi.