1
Inã rantsuwa da hantsi.
2
Da dare a lõkacin da ya rufe (da duhunsa).
3
Ubangijinka bai yi maka bankwana ba, kuma bai ƙĩ kaba.
4
Kuma lalle ta ƙarshe ce mafi alheri a gare ka daga ta farko.
5
Kuma lalle ne, Ubangijinka zai yi ta bã ka kyauta sai ka yarda.
6
Ashe, bai sãme ka marãya ba, sa'an nan Ya yi maka makõma?
7
Kuma Ya sãme ka bã ka da shari'ã, sai Ya shiryar da kai?
8
Kuma Ya sãme ka matalauci, sai Ya wadãtã ka?
9
Sabõda haka, amma marãya, to, kada ka rinjãye shi.
10
Kuma amma mai tambaya, kada ka yi masa tsãwa.
11
Kuma amma ni'imar Ubangijinka, sai ka faɗa (dõmin gõdiya).