All Islam Library

55 - The Beneficent - Ar-Raĥmān

:1

(Allah) Mai rahama.

:2

Yã sanar da Alƙur'ani.

:3

Yã halitta mutum.

:4

Yã sanar da shi bayãni (magana).

:5

Rãnã da watã a kan lissãfi suke.

:6

Kuma tsirrai mãsu yãɗo da itãce sunã tawãlu'i.

:7

Kuma samã Ya ɗaukaka ta, Kuma Yã aza sikẽli.

:8

Dõmin kada ku karkatar da sikẽlin.

:9

Kuma ku daidaita awo da ãdalci, kuma kada ku rage sikẽlin.

:10

Kuma ƙasã Yã aza ta dõmin tãlikai.

:11

A cikinta akwai 'ya'yan itãcen marmari da dabĩno mai kwasfa.

:12

Da ƙwãya mai sõshiya da ƙamshi.

:13

To, sabõda wanne daga ni'imõmin Ubangjinku kuke ƙaryatãwa?

:14

Yã halitta mutum daga ƙẽkasasshen yumɓu kumar kasko.

:15

Kuma ya halitta aljani daga bira daga wutã.

:16

To, sabõda wanne daga ni'imõmin Ubangijinku, kuke ƙaryatãwa?

:17

Ubangjin mafita biyu na rãnã, kuma Ubangijin mafãɗã biyu na rãnã.

:18

To, sabõda wanne daga ni'imõmin Ubangijinku, kuke ƙaryatãwa?

:19

Yã garwaya tẽku biyu (ruwan dãɗi da na zartsi) sunã haɗuwa.

:20

A tsakãninsu akwai shãmaki, bã za su ƙetare haddi ba.

:21

To, sabõda wanne daga ni'imõmin Ubangijinku, kuke ƙaryatãwa?

:22

Lu'ulu'u da murjãni na fita daga gare su.

:23

To, sabõda wanne daga ni'imõmin Ubangijinku, kuke ƙaryatãwa?

:24

Kuma Yanã da manyan jirãge, waɗanda ake ƙãgãwa a cikin tẽku kamar manyan duwãtsu.

:25

To, sabõda wanne daga ni'imõmin Ubangijinku, kuke ƙaryatãwa?

:26

Dukkan wanda ke kanta mai ƙãrẽwa ne.

:27

Kuma Fuskarar Ubangijinka, Mai girman Jalala da karimci, ita ce take wanzuwa.

:28

To, sabõda wanne daga ni'imõmin Ubangijinku, kuke ƙaryatãwa?

:29

wanda ke a cikin sammai da ƙasã yanã rõƙon Sa (Allah), a kullum Allah na a cikin wani sha'ani.

:30

To, sabõda wanne daga ni'imõmin Ubangijinku, kuke ƙaryatãwa?

:31

Zã mu ɗauki lõkaci sabõda ku, yã kũ mãsu nauyin halitta biyu!

:32

To, sabõda wanne daga ni'imõmin Ubangijinku, kuke ƙaryatãwa?

:33

Ya jama'ar aljannu da mutãne! Idan kunã iya zarcẽwa daga sãsannin sammai da ƙasã to ku zarce. Bã za ku iya zarcẽwaba fãce da wani dalĩli.

:34

To, sabõda wanne daga ni'imõmin Ubangijinku, kuke ƙaryatãwa?

:35

Anã sako wani harshe daga wata wutã a kanku, da narkakkiyar tagulla. To, bã zã ku nẽmi taimako ba?

:36

To, sabõda wanne daga ni'imõmin Ubangijinku, kuke ƙaryatãwa?

:37

Sa'an nan idan sama ta tsãge kuma ta zama jã kamar jar fãta.

:38

To, sabõda wanne daga ni'imõmin Ubangijinku, kuke ƙaryatãwa?

:39

To, a ran nan bã zã a tambayi wani mutum laifinsa ba, kuma haka aljani.

:40

To, sabõda wanne daga ni'imõmin Ubangijinku, kuke ƙaryatãwa?

:41

zã a iya sanin mãsu laifi da alãmarsu, sabõda haka sai a kãma kwarkaɗarsu da sãwãyensu.

:42

To, sabõda wanne daga ni'imõmin Ubangijinku, kuke ƙaryatãwa?

:43

Wannan Jahannama ce wadda mãsu laifi ke ƙaryatãwa game da ita.

:44

Sunã kẽwaya a tsakaninta da ruwan ɗimi mai tsananin tafasa.

:45

To, sabõda wanne daga ni'imõmin Ubangijinku, kuke ƙaryatãwa?

:46

Kuma wanda ya ji tsõron tsayãwa a gaba ga Ubangijinsa yanã da Aljanna biyu.

:47

To, sabõda wanne daga ni'imõmin Ubangijinku, kuke ƙaryatãwa?

:48

Mãsu rassan itãce.

:49

To, sabõda wanne daga ni'imõmin Ubangijinku, kuke ƙaryatãwa?

:50

A cikinsu akwai marẽmari biyu sunã gudãna.

:51

To, sabõda wanne daga ni'imõmin Ubangijinku, kuke ƙaryatãwa?

:52

A cikinsu akwai nau'i biyu daga kõwane 'ya'yan itãcen marmari.

:53

To, sabõda wanne daga ni'imõmin Ubangijinku, kuke ƙaryatãwa?

:54

Sunã gincire a kan waɗansu shimfiɗu cikinsu tufãfin alharĩni mai kauri ne kuma nũnannun 'yã'yan itãcen Aljannar biyu kusakusa suke.

:55

To, sabõda wanne daga ni'imõmin Ubangijinku, kuke ƙaryatãwa?

:56

A cikinsu akwai mãtã mãsu taƙaita ganinsu, wani mutum, gabanin mazajensu bai ɗebe budurcinsu ba kuma haka wani aljani.

:57

To, sabõda wanne daga ni'imõmin Ubangijinku, kuke ƙaryatãwa?

:58

Kamar dai su yaƙũtu ne da murjãni.

:59

To, sabõda wanne daga ni'imõmin Ubangijinku, kuke ƙaryatãwa?

:60

Shin, kyautatãwa nã da wani sakamako? (Ã'aha) fãce kyautatãwa.

:61

To, sabõda wanne daga ni'imõmin Ubangijinku, kuke ƙaryatãwa?

:62

Kuma baicinsu akwai waɗansu gidãjen Aljanna biyu.

:63

To, sabõda wanne daga ni'imõmin Ubangijinku, kuke ƙaryatãwa?

:64

Mãsu duhun inuwa.

:65

To, sabõda wanne daga ni'imõmin Ubangijinku, kuke ƙaryatãwa?

:66

A cikinsu akwai marẽmari biyu masu kwarãrar ruwa.

:67

To, sabõda wanne daga ni'imõmin Ubangijinku, kuke ƙaryatãwa?

:68

A cikinsu akwai 'ya'yan itãcen marmari da dabĩno darummãni.

:69

To, sabõda wanne daga ni'imõmin Ubangijinku, kuke ƙaryatãwa?

:70

A cikinsu, akwai wasu mãtã mãsu kyaun hãlãye, mãsu kyaun halitta.

:71

To, sabõda wanne daga ni'imõmin Ubangijinku, kuke ƙaryatãwa?

:72

Mãsu farin idãnu da baƙinsu waɗanda aka tsare a cikin haimõmi.

:73

To, sabõda wanne daga ni'imõmin Ubangijinku, kuke ƙaryatãwa?

:74

Wani mutum, gabanin mazajensu bai ɗẽbe budurcinsu ba, kuma haka wani aljani.

:75

To, sabõda wanne daga ni'imõmin Ubangijinku, kuke ƙaryatãwa?

:76

Sunã gincire a kan wasu matãsai mãsu kõren launi da katĩfun Abkara kyãwãwa.

:77

To, sabõda wanne daga ni'imõmin Ubangijinku, kuke ƙaryatãwa?

:78

Sũnan Ubangjinka, Mai girman Jalãla da Karimci, ya tsarkaka.