1
Mai ƙwanƙwasar (zukata da tsõro)!
2
Mẽnẽ ne mai ƙwanƙwasa?
3
Kuma me ya sanar da kai abin da ake ce wa mai ƙwanƙwasa?
4
Rãnar da mutãne za su kasance kamar 'ya'yan fari mãsu wãtsuwa.
5
Kuma duwãtsu su kasance kamar gãshin sũfin da aka saɓe.
6
To, amma wanda ma'aunansa suka yi nauyi.
7
To, shi yana a cikin wata rayuwa yardadda.
8
Kuma amma wanda ma'aunansa suka yi sauƙi (bãbu nauyi).
9
To, uwarsa Hãwiya ce.
10
Kuma me ya sanar da kai mece ce ita?
11
Wata wuta ce mai zafi.