1
Ina rantsuwa da dawãki mãsu gudu suna fitar da kũkan ciki.
2
Mãsu ƙyasta wuta (da kõfatansu a kan duwatsu) ƙyastawa.
3
Sa'an nan mãsu yin hari a lokacin asuba.
4
Sai su motsar da ƙũra game da shi.
5
Sai su shiga, game da ita (ƙũrar), a tsakãnin jama'ar maƙiya.
6
Lalle ne mutum mai tsananin butulci ne ga Ubangijinsa.
7
Lalle ne shi mai shaida ne a kan laifinsa dl haka.
8
Kuma 1alle ne ga dũkiya shi mai tsananin so ne.
9
Shin, bã ya da sanin lõkacin da aka tõne abin da yake cikin kaburbura.
10
Aka bayyana abin da ke cikin zukata.
11
Lalle ne Ubangijinsu, game da su a ranar nan Mai ƙididdigewa ne?