1
Idan aka girgiza ƙasa, girgizawarta.
2
Kuma ƙasa ta fitar da kayanta, masu nauyi.
3
Kuma mutum ya ce "Mẽ neya same ta?"
4
A rãnar nan, zã ta faɗi lãbãrinta.
5
cewa Ubangijinka Ya yi umurni zuwa gare ta.
6
A rãnar nan mutane za su fito dabam-dabam domin a nuna musu ayyukansu.
7
To, wanda ya aikata (wani aiki) gwargwadon nauyin zarra, na alheri, zai gan shi.
8
Kuma wanda ya aikata gwargwadon nauyin zarra na sharri, zai gan shi.