1
Alfahari da yawan dũkiya da dangi ya shagaltar da ku (dagaibada mai amfaninku).
2
Har kuka ziyarci kaburbura.
3
A'aha! (Nan gaba) zã ku sani.
4
Sa'an nan, tabbas, zã ku sani.
5
Haƙĩƙa, da kuna da sani sani na yaƙĩni.
6
Lalle ne da kuna ganin Jahĩm.
7
Sa'an nan lalle ne za ku gan ta, da idanu, bayyane.
8
Sa'an nan lalle ne za a tambaye ku, a rãnar nan lãbãrin ni'imar (da aka yi muku).