All Islam Library

89 - The Dawn - Al-Fajr

:1

Inã rantsuwa da alfijiri.

:2

Da darũruwa gõma.

:3

Da (adadi na) cikã da (na) mãrã.

:4

Da dare idan yana shũɗewa.

:5

Ko a cikin waɗannan akwai abin rantsuwa ga mai hankali (da yake kange shi daga zunubi)?

:6

Ba ka ga yadda Ubangijinka Ya aikata da Ãdãwa ba?

:7

Iramawa mãsu sakon ƙĩrar jiki.

:8

Waɗanda ba a halitta kwatankwacinsu ba a cikin garũruwa (na dũniya).

:9

Da samũdãwa waɗanda suka fasa duwãtsu a cikin Wadi suka yi gidãje)?

:10

Da Fir'auna mai turãku.

:11

Waɗanda suka ƙẽtare iyãkarsu, a cikin garũruwa?

:12

Sabõda haka, suka yawaita yin ɓarna a cikinsu.

:13

Sabõda haka Ubangijinka Ya zuba musu bũlãlar azãba.

:14

Lalle ne, Ubangijinka Yana nan a mafaka.

:15

To, amma fa mutum idan Ubangijibsa Ya jarraba shi, wãto Yã girmama shi kuma Ya yi masa ni'ima, sai ya ce: "Ubangijina Ya girmama ni."

:16

Kuma idan Ya jarraba shi, wãto Ya ƙuntata masa abincinsa, sai ya ce: "Ubangijina Ya walãkanta ni."

:17

A'aha! Bari wannan, ai bã ku girmama marãya!

:18

Bã ku kwaɗaitã wa jũnanku ga (tattalin) abincin matalauci!

:19

Kuma kuna cin dũkiyar gãdo, ci na tãrãwa.

:20

Kuma kuna son dũkiya, so mai yawa.

:21

A'aha! Idan aka niƙa ƙasa niƙewa sosai.

:22

Kuma Ubangijinka Ya zo, alhãli malã'iku na jẽre, safũ- safu.

:23

Kuma a ranar nan aka zo da Jahannama. A ranar nan mutum zai yi tunãni. To, inã fa tunãni yake a gare shi!

:24

Yana dinga cẽwa, "Kaitona, dã na gabatar (da aikin ƙwarai) domin rãyuwata!"

:25

To, a rãnar nan bãbu wani mai yin azãba irin azãbar Allah.

:26

Kuma bãbu wani mai ɗauri irin ɗaurinSa.

:27

Yã kai rai mai natsuwa!

:28

Ka koma zuwa ga Ubangijinka, alhãli kana mai yarda (da abin da Ya ƙaddara maka a dũniya) abar yardarwa (da sakamakon da zã a ba ka a Lãhira).

:29

Sabõbda haka, ka shiga cikin bãyiNa (mãsu bin umurui a dũniya).

:30

Kuma ka shiga AljannaTa (a Lãhira).