All Islam Library

86 - The Nightcommer - Aţ-Ţāriq

:1

Inã rantsuwa da sama da mai aukõwa da dare.

:2

To, mẽ yã sanar da kai abin da ake cẽwa mai aukõwa da dare?

:3

Shi ne taurãron nan mai tsananin haske.

:4

Bãbu wani rai fãce a kansa akwai wani mai tsaro.

:5

To, mutum ya dũba, daga mẽ aka halittã shi?

:6

An halittã shi daga wani ruwa mai tunkuɗar jũna.

:7

Yanã fita daga tsakanin tsatso da karankarman ƙirji.

:8

Lalle ne Shi (Allah), ga mayar da shi (mutum), tabbas Mai iyãwa ne.

:9

Rãnar da ake jarrabawar asirai.

:10

Saboda haka, bã shi da wani ƙarfi, kuma bã shi da wani mai taimako (da zai iya kãre shi daga azãbar Allah).

:11

Ina rantsuwa da sama ma'abũciyar ruwa mai kõmãwa yana yankẽwa.

:12

Da ƙasa ma'abũciyar tsãgẽwa,

:13

Lalle ne shĩ (Alƙur'ãni), haƙĩƙa magana ce daki-daki

:14

Kuma shĩ bã bananci bane

:15

Lalle ne sũ, suna ƙulla kaidi na sõsai.

:16

Kuma Ni, Ina mayar da kaidi (gare su) kamar yadda suke ƙulla kaidi.

:17

Saboda haka, ka yi wa kafirai jinkiri, ka dakata musu, sannu-sannu.