All Islam Library

85 - The Mansions of the Stars - Al-Burūj

:1

Inã rantsuwa da sama mai taurãrin lissafin shekara.

:2

Da yinin da aka yi alkawarin zuwansa,

:3

Da yini mai shaidu, da yini da ake halarta a cikinsa

:4

An la'ani mutãnen rãmi.

:5

Wato wuta wadda aka hura.

:6

A lõkacin da suke a kan (gefen) ta a zazzaune.

:7

Alhãli sũ, bisa ga abin da suke aikatãwa ga mũminai, sunã halarce.

:8

Kuma ba su tuhumce su ba, fãce kawai domin sun yi ĩmãni da Allah Mabuwãyi, wanda ake gõdewa.

:9

Wanda Yake shi ne da mulkin sammai da ƙasa, kuma Allah a kan kõme halarce Yake.

:10

Lalle ne waɗanda suka fitini mũminai maza da mũminai mãta, sa'an nan ba su tũba ba to, sunã da azãbar Jahannama, kuma sunã da azãbar gõbara.

:11

Lalle ne waɗanda suka yi ĩmãni, kuma suka aikata ayyukan ƙwarai, sunã da gidãjen Aljanna, ƙoramu na gudãna daga ƙarƙashin gidãjen. Wancan abu fa shi ne rabo babba.

:12

Lalle ne damƙar Ubangijinka mai tsanani ce ƙwarai.

:13

Lalle ne Shĩ, Shi ne Mai ƙãga halitta, kuma Ya mayar da ita (bãyan mutuwa).

:14

Kuma Shi ne Mai gãfara, Mai bayyana sõyayya.

:15

Mai Al'arshi mai girma

:16

Mai aikatãwa ga abin da Yake nufi.

:17

Ko lãbãrin rundanõni yã zo maka.

:18

Fir'auna da samũdãwa?

:19

Ã'aha! waɗanda suka kãfirta sunã cikin ƙaryatãwa.

:20

Alhãli, Allah daga bãyansu, Mai kẽwaye su ne (da saninSa).

:21

Ã'aha! Shi Alƙur'ãni ne mai girma.

:22

A cikin Allo tsararre.