1
Bone ya tabbata ga duk mai nune, mai zunɗe (mai raɗa).
2
Wanda ya tara dũkiya, kuma ya mayar da ita abar tattalinsa.
3
Yana zaton cẽwa dũkiyarsa za ta dawwamar da shi.
4
A'aha! Lalle ne zã a jẽfa shi a cikin Huɗama.
5
Kuma me ya sanar da kai abin da ake ce wa Huɗama?
6
Wutar Allah ce wadda ake hurawa.
7
Wadda take lẽƙãwa a kan zukata.
8
Lalle ne ita abar kullẽwa cea kansu.
9
A cikin wasu ginshiƙai mĩƙaƙƙu.