All Islam Library

83 - The Defrauding - Al-Muţaffifīn

:1

Bone ya tabbata ga mãsu naƙƙasãwa.

:2

Waɗanda suke idan suka auna daga mutãne suna cika mũdu.

:3

Kuma idan sun auna musu da zakka ko da sikẽli, suna ragẽwa

:4

Ashe! Waɗancan bã su tabbata cẽwa lalle sũ, ana tãyar da su ba?

:5

Domin yini mai girma.

:6

Yinin da mutãne ke tãshi zuwa ga Ubangijin halitta?

:7

Haƙĩƙa lalle ne littãfin fãjirai dãhir, yana a cikin Sijjĩn.

:8

Kuma, mẽ ya sanar da kai abin da akẽ cẽ wa Sijjĩn?

:9

Wani 1ittãfi ne rubũtacce.

:10

Bone yã tabbata a rãnar nan ga mãsu ƙaryatãwa.

:11

Waɗanda suke ƙaryatãwa game da rãnar sakamako.

:12

Babũ mai ƙaryatãwa gare shi fãce dukan mai ƙẽtare haddi mai yawan zunubi.

:13

Idan ana karãtun ãyõyinmu, a kansa, sai ya ce: tãtsũniyõyin mutãnen farko ne.

:14

A'aha! Bã haka ba, abin da suka kasance suna aikatãwa dai, yã yi tsãtsa a cikin zukãtãnsu.

:15

A'aha! Haƙĩƙa, lalle ne sũ daga Ubangijinsu, rãnar nan, waɗanda ake shãmakancẽwa ne.

:16

Sa'an nan, lalle ne, sũ mãsu shiga cikin Jahĩm ne.

:17

Sa'an nan a ce: "Wannan shi ne abin da kuka kasance kuna ƙaryatãwa game da shi."

:18

A'aha! Haƙĩƙa lalle ne littãfin mãsu ɗã'ã yana a cikin Illiyyĩna?

:19

Kuma mẽne ne yã sanar da kai abin da ake cẽwa Illiyyũna?

:20

Wani littãfi ne rubũtacce.

:21

Muƙarrabai suke halarta shi.

:22

Lalle ne, mãsu ɗã'ã ga Allah tabbas suna cikin ni'ima.

:23

A kan karagu, suna ta kallo.

:24

Kana sani a cikin huskõkinsu, akwai kwarjinin ni'ima.

:25

Ana shãyar da sũ daga wata giya wadda aka yunƙe a kan rufinta.

:26

¡arshen kurɓinta miski ne. To, a cikin wannan, mãsu gwagwarmaya su yi ta gwagwarmayar nẽma.

:27

Kuma abin da ake gauraya ta da shi, daga tasnĩm yake.

:28

(Wato) wani marmaro ne wanda muƙarrabai ke sha daga gare shi.

:29

Lalle ne, waɗanda suka kãfirta sun kasance (a dũniya) suna yi wa waɗanda suka yi ĩmãni dãriya.

:30

Kuma idan sun shuɗe su sai su dinga yin zunɗe.

:31

Kuma idan suka jũya zuwa ga iyãlansu, sai su tafi suna kãkãci.

:32

Kuma idan sun gan su sai su ce: "Lalle waɗannan ɓatattu ne."

:33

Alhãli kuwa, ba a aike su ba dõmin su zama mãsu tsaro a kansu.

:34

To, yau fa (a Lãhira] waɗanda suka yi ĩmãni, sũ ke yi wa kãfirai dãriya.

:35

A kan karagu, suna ta kallo.

:36

Shin an sãka ma kãfirai abin da suka kasance suna aikatawa?