All Islam Library

44 - The Smoke - Ad-Dukhān

:1

Ḥ. M̃.

:2

Inã rantsuwa da Littãfi Mabayyani.

:3

Lalle ne, Mũ, Muka saukar da shi a cikin wani dare mai albarka. Lalle Mũ' Mun kasance Mãsu yin gargaɗi.

:4

A cikinsa (shi daren) ake rarrabe kõwane umurui bayyananne.

:5

Umurni na daga wurinMu. Lalle Mũ ne Muka kasanceMãsu aikãwã.

:6

Sabõda rahama daga Ubangijinka. Lalle Shĩ, Shi ne Mai ji, Mãsani.

:7

(Shĩ ne) Ubangijin sammai da ƙasa da abin da ke a tsakãninsu, idan kun kasance mãsu yaƙĩni (za ku gãne haka).

:8

Babu abin bautãwa fãce Shi. Yana rãyarwa Kuma Yana kashẽwa. (Shi ne) Ubangijinku, kuma Ubangijin ubanninku na farko.

:9

A'a sũ, sunã wãsã a cikin shakka.

:10

Sabõda haka, ka dakata rãnar da sama zã tã zo da hayãƙi bayyananne.

:11

Yanã rufe mutãne. Wannan wata azãba ce mai raɗaɗi.

:12

Ya Ubangijinmu! Ka kuranye mana azãba. Lalle Mũ, mãsu ĩmãni ne.

:13

Inã tunãwa take a gare su, alhãli kuwa, haƙĩƙa, Manzo mai bayyanãwa Ya je musu (da gargaɗin saukar azãbar, ba su karɓa ba)?

:14

Sa'an nan suka jũya baya daga gare shi, Kuma suka ce: "Wanda ake gayãwa ne, mahaukaci."

:15

Lalle Mũ, Mãsu kuranyẽwar azãba ne, a ɗan lõkaci kaɗan, lalle kũ, mãsu kõmãwa ne (ga laifin).

:16

Rãnar da Muke damƙa, damƙa mafi girma, lalle ne Mũ mãsu azãbar rãmuwa ne.

:17

Kuma lalle ne haƙĩƙa a gabaninsu, Mun fitini mutãnen Fir'auna, kuma wani Manzo karĩmi ya jẽ musu.

:18

(Mazon ya ce): "Ku kãwo mini (ĩmãninku) ya bayin Allah! Lalle ni, Manzo ne amintacce zuwa gare ku."

:19

"Kuma kada ku nẽmi ɗaukaka a kan Allah. Lalle nĩ mai zo muku ne da dalĩli bayyananne."

:20

"Kuma lalle nĩ na nẽmi tsari da Ubangijĩna, kuma Ubangijinku, dõmin kada ku jẽfe ni."

:21

"Kuma idan ba ku yi ĩmãni sabõda nĩ ba, to, ku nĩsance ni."

:22

Sai ya kirayi Ubangjinsa cẽwa waɗannan mutãnene mãsu laifi.

:23

(Allah Ya ce): "To, ka yi tafiyar dare da bayiNa, da dare. Lalle kũ, waɗanda ake bĩ ne (dõmin a kãma ku.)"

:24

"Kuma ka bar tẽku rarrabe. Lalle sũ, runduna ce abar nutsarwa."

:25

Da yawa suka bar gõnaki da marẽmari.

:26

Da shuke-shuke da matsayi mai kyau.

:27

Da wata ni'ima da suka kasance a cikinta sunã mãsu hutu.

:28

Kamar haka! Kuma Muka gãdar da ita ga waɗansu mutãne na dabam.

:29

Sa'an nan samã da ƙasã ba su yi kũka a kansu ba, Kuma ba su kasance waɗanda ake yi wa jinkiri ba.

:30

Kuma lalle ne, haƙĩƙa Mun tsĩrar da Banĩ Isrã'ĩla daga, azãba mai wulãkantãwa.

:31

Daga Fir'auna. Lalle shi, ya kasance maɗaukaki daga cikin mãsu ɓarna.

:32

Kuma lalle ne, haƙĩƙa, Mun zãɓe su sabõda wani ilmi (na Taurata) a kan mutãne.

:33

Kuma Muka bã su, daga ãyõyin mu'ujizõji, abin da yake a cikinsa, akwai ni'ima bayyananna

:34

Lalle waɗannan mutãne, haƙĩka, sunã cẽwa,

:35

"Babu wani abu sai mutuwarmu ta farko, kuma ba mu zama waɗanda ake tãyarwa ba."

:36

"Sai ku zo da ubanninmu, idan kun kasance mãsu gaskiya."

:37

shin, sũ ne mafĩfĩta kõ kuwa mutãnen Tubba'u, kuma da waɗanda ke a gabãninsu? Mun halaka su, lalle sũ, sun kasance mãsu laifi.

:38

Kuma ba Mu halitta slmmai da ƙasa da abin da ke a tsakãninsu ba, alhãli kuwa Munã mãsu wãsã.

:39

Ba Mu halitta su ba fãce da manufa ta gaskiya, kuma amma mafi yawansu, ba su sani ba.

:40

Lalle rãnar rarrabẽwa, ita ce lõkacin wa'adinsu gabã ɗaya.

:41

Rãnar da wani zumu bã ya amfãnin wani zumu da kõme kuma ba su zama anã taimakon su ba.

:42

fãce wanda Allah Ya yi wa rahama. Lalle Shi (Allah), shĩ ne Mabuwãyi, Mai jin ƙai.

:43

Lalle itãciyar zaƙƙũm (ɗanyen wutã),

:44

Ita ce abincin mai laifi.

:45

Kamar narkakken kwalta yanã tafasa a cikin cikunna.

:46

Kamar tafasar ruwan zãfi.

:47

(A cẽ wa malã'ikun wutã), "Ku kãmã shi, sa'an nan ku fizge shi zuwa ga tsakiyar Jahĩm."

:48

"Sa'an nan ku zuba, a kansa, daga azãbar ruwan zãfi."

:49

(A ce masã), "Ka ɗanɗana! Lalle kai, kai ne mabuwãyi mai girma!"

:50

"Lalle wannan, shi ne abin da kuka kasance kunã shakka game da shi."

:51

Lalle mãsu taƙawa sunã cikin matsayi amintacce.

:52

A cikin gidãjen Aljanna da marẽmari.

:53

Sunã tufanta daga tufãfin alharĩni raƙĩƙi, da mai kauri, sunã mãsu zaman fuskantar jũna.

:54

Kamar haka, kuma Mun aurar da su da mãtã mãsu kyaun idãnu, mãsu girmansu.

:55

Sunã kira, a cikinsu (gidẽjen) ga dukan 'ya'yan itãcen marmari, sunã amintattu (daga dukan abin tsõro).

:56

Bã su ɗanɗanar mutuwa, a cikinsu, fãce mutuwar farko, kuma (Allah), Ya tsare musu azãbar Jahĩm.

:57

Sabõda falala daga Ubangijinka. Wancan shi ne babban rabo, mai girma.

:58

Dõmin haka kawai Muka sauƙaƙar da shi (Alƙur'ãni) da harshenka, tsammãninsu, su riƙa tunãwa.

:59

Sai ka yi jira. Lalle sũ, mãsu jira ne.