1
Ka ce: "Ya kũ kãfirai!"
2
"Bã zan bautã wa abin da kuke bautã wa ba."
3
"Kuma kũ, ba ku zama masu bauta wa abin da nake bautã wa ba."
4
"Kuma nĩ ban zama mai bautã wa abin da kuka bautã wa ba."
5
"Kuma kũ, ba ku zama mãsu bautã wa abin da nake bautã wa ba."
6
"Addininku na garẽ ku, kuma addinina yanã gare ni."